Ba tabbacin zaman Ronaldo a Real Madrid

cristiano ronaldo
Image caption Cristiano Ronaldo na son sake daukar Kofin Zakarun Turai

Cristiano Ronaldo ya ce bai sani ba ko zai cigaba da zama a Real Madrid bayan kwantiragin sa ko kuma zai bar su.

Ronaldo mai shekara 27 ya ce a yanzu babu wata tantama zai cigaba da zama a Bernabeu har zuwa 2015 karshen kwantiragin sa na yanzu amma kuma daga nan ba shi da wani tabbaci na abin da zai biyo baya.

Dan wasan ya yi kalaman ne sakamakon furucin da ya yi a watan Satumba cewa shi kam jikinsa ya yi la'asar game da kungiyar tasa.

Dan wasan wanda ya roki magoya bayan kungiyar da su kara hakuri da kocin su Jose Mourinho, ya ce yanzu abin da suka maida hankalin su a kai shi ne kofin Zakarun Turai da suke fatan dauka karo na goma.

Sai dai ya ce ba abu ne mai sauki ba, amma kuma su na da kwarin guiwa sosai a kai.

Karin bayani