Na yi amfani da kwayoyi —Armstrong

Lance Armstrong
Image caption Lance Armstrong ya amince cewa ya yi amfani da kwayoyi

Wasu majiyoyi sun shaidawa kafofin yada labarai na Amurka cewa dan wasan tseren keken nan Lance Armstrong ya amince cewa ya yi amfani da kwayoyi masu kara kuzari.

A bara ne dai hukumar hana amfani da kwayoyi a harkar wasanni ta Amurka (Usada) ta zarge shi da abin da ta kira "dabara mafi nasara ta zamani ta amfani da kwayoyi" a tarihin wasan tseren keke.

Kafin yanzu dai Armstrong, mai shekaru 41, ya tsaya kai-da-fata cewa shi bai aikata laifi ba.

Wasu majiyoyi dake da masaniya a kan wata hira da ya yi da shahararriyar ma'aikaciyar talabijin din nan Oprah Winfrey—hirar da za a yada ranar Alhamis—sun shaidawa jaridun Amurka cewa ya amince cewa ya yi amfani da kwayoyi.

Sai dai a cewar majiyar New York Times, ya musanta cewa shi ne jagoran shirin amfani da kwayoyin.