An ce Armstrong ya amsa laifinsa

Lance Armstrong da Oprah Winfrey
Image caption An ce Armstrong ya amsa laifi a shirin Oprah

Shahararren dan tseren keke na duniya Lance Armstrong ya mince cewa ya yi amfani da kwayoyin kara kuzari a wata hirar talabijin da aka yi da shi a shirin nan na Oprah Winfrey , wanda za a nuna ranar Alhamis, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

A shekarar da ta wuce Hukumar hana amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni ta Amurka (Usada) ta zargi

Armstrong da aikata abin da ta kira surkullen amfani da kwayoyi mafi nasara a wasanni a duniya.

Kafin yanzu Armstrong dan shekara 41 ya sha musanta aikata laifin amfani da kwayoyin.

Rahotan amsa laifin nasa da ake cewa ya yi a hirar ta shrin na Oprah ta Amurka ya zo ne sa'oi bayan Armstrong din

ya nefi gafarar ma'aikatan Asusunsa na gudanar da ayyukan jinkai amma kuma bai fito fili ya amsa laifin ba.

An karbe lambobi bakwai na gasar tseren keke ta Faransa, Tour de France da ya samu.