Guardiola zai koma Premier

pep guardiola
Image caption Pep Guardiola na sha'awar tafiya gasar Premier

Tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce zai koma Ingila a kakar wasanni mai zuwa domin horadda wata kungiyar gasar Premier.

Kocin mai shekara 41 wanda ya jagoranci Barcelona ta dauki kofuna 14 a kakar wasanni 4 ya na neman sabon klub a yanzu.

Ya ce lokacin da ya ke buga wasa bai samu damar cimma burinsa na yin wasa a Ingila ba a wata kungiya amma a yanzu yana fatan cimma wannan buri a matsayin koci.

Kalaman nasa dai ana ganin za su yi wa kungiyoyin Manchester City da United da kuma Chelsea wadanda ake ganin su na bukatarsa.

Guardiolan ya bayyana aniyar tasa ce ta zuwa Ingilan bayan Jose Mourinho ya sanar da kudirinsa na sake komawa gasar Premier a karshen wa'adin kwantiraginsa da Real Madrid.

Guardiola ya ce gasar Premier ta na bashi sha'awa, gasa ce ta dabam.

Ya ce ya na son ta saboda yanayinta da magoya bayan kungiyoyin wadanda komai wuya komai dadi su na tare da mai horadda 'yan wasansu.

Ya ce saboda haka ya ke son samun damar zuwa can.

A wasu lokutan dai an ruwaito cewa kungiyoyin Bayern Munich da AC Milan na neman kocin wanda ya ajiye aikinsa da Barcelona a 2012.

A yanzu Guardiola ya na zaune ne a New York da iyalansa bayan da ya dauki hutun shekara daya daga harkar wasan kwallon kafa.

A wani sakon fatan alheri na bidiyo da ya aikewa Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila kan bikin cikar ta shekara 150 da kafuwa, kocin ya yabawa Hukumar kan cimma wannan lokaci tare da yaba mata wajen bunkasa wasan kwallon kafa.

Karin bayani