An hana Tevez tuka mota

carlos tevez
Image caption Carlos Tevez ya ce bai san ma'anar kalmar kwanstabulari ba

An haramtawa Tevez tuka mota har tsawon watanni 6 bayan da ya ki amsa wasikar 'yan sanda ta tuhumarsa da laifin gudun da ya wuce ka'ida.

Dan wasan ya ce bai fahamci cewa takardun tuhumar tasa da laifin daga 'yan sanda suke ba shi yasa bai amsa ba saboda an yi amfani ne da wata kalma ta kwanstabulari maimakon ainahin kalmar ingilishi ta police dake nufin dan sanda a don haka bai gane turancin ba.

Tevez ya amince da aikata laifin kasa baiwa 'yan sanda bayanai a kotun Majistare ta Manchester, amma kuma ya musanta cewa ya na tuki ne lokacin da malejin motarsa ya nuna cewa yana gudun da ya wuce ka'ida har sau biyu.

Lauyansa Gwyn Lewis ya shedawa kotun cewa Tevez din ya san kalmar police wadda ke nufin dan sanda amma fa ba wata kalma ba kuma ta dabam mai sarkakiya.

Ya ce a dukkanin wasikun ba bu inda aka yi amfani da kalmar police.

Kotun ta ci tarar dan wasan fam 1,540.

A watan Nuwamba da ya wuce kotun Majistare ta Lancaster ta haramta mi shi tuka mota na wucin gadi saboda rashin bada bayani bayan malejin motarsa ya nuna cewa ya na gudun da ya zarta ka'ida har sau biyu a watan Maris na 2012.

A watan Satumba na 2012 ma an ci tararsa fam 60 tare da wadansu hukunce-hukuncen uku a kan lasisinsa na tuki bayan da ya amince da tukin da ya zarta ka'ida.

A ya yin zaman kotu a lokacin ya amince da aikata laifin amma ya ce bai ga takardar tuhumar sa da laifin ba, shi yasa ya yi burus, akan cewa bai ga takardara ba kotun ta bar tuhumar.

Karin bayani