Ba dan gasar Premier a zakarun UEFA

michel platini
Image caption Michel Platini shugaban Hukumar uefa da ba bu dan premier a zakarunta

Hukumar kwallon Kafa ta Turai, UEFA ta sanar da jerin sunayen 'yan wasanta na shekara ta 2012 kuma a karon farko ba bu dan gasar Premier.

Kuri'a miliyan biyar da dubu dari uku aka kada a zaben 'yan wasan karo na 12 a shafin intanet na Hukumar ta Uefa.

An sami karin kashi ashirin cikin dari kan na shekarar da ta wuce.

'yan wasa takwas ne daga gasar La Liga aka zaba, hudu-hudu daga kungiyoyin Barcelona da Real Madrid.

Jerin gwanayen 'yan wasan na Uefa dai ba hukumar ba ce ta ke zaben su da kanta magoya bayan kungiyoyi ne su ke zaben a shafinta na intanet kuma a shekaru 11 ya samu farin jini da kuri'u miliyan 24.

A 2001 lokacin da aka fara zaben ya hada da Sami Hyypia na Liverpool da 'yan wasan Arsenal Patrick Vieira da Thierry Henry da David Beckam na Manchester United da kuma Gareth Bale na Tottenham wanda a bara ma an zabe shi.

A zaben na bana an saka gwarzon dan wasan duniya Lionel Messi a karo na biyar a jere, ya yin da aka zabi Cristiano Ronaldo da Iker Casillas na Real Madrid karo na shida a jere.

An kuma bukaci masu ziyartar shafin na intanet na Uefa kan su zabi tsarin wasan da ya fi kyau su ka zabi 4-4-2.

Sunayen 'yan wasan

Iker Casillas(Real Madrd), Sergio Ramos (Real Madrid), Gerard Pique(Barcelona), Thiago Silva (AC Milan/ Paris St-Germaine), Philipp Lahm (Bayern Munich), Andres Iniesta (Barcelona) , Xavi Hernandez (Barcelona), Andrea Pirlo (Juventus) , Mesut Ozil (Real Madrid), Lionel Messi (barcelona), Cristiano Ronaldo (Real Madrid).

Gwanayen 'yan wasan FIFA na shekara da aka zaba na 2012 ya kunshi 'yan wasan gasar La Liga ne kawai.