An karbe wa Armstrong lambar Olympics

lance armstrong
Image caption Lance Armstrong ya yi hira da Oprah Winfrey

Kwamitin wasan Olympics na Duniya ya karbe lambar yabo ta tagulla da shahararren dan tseren keken nan Lance Armstrong ya samu a gasar Olympics ta Sydney ta 2000.

Kwamitin wasan Olympics din ya dauki wannan mataki ne bayan Hukumar Tseren keke ta Duniya (UCI) ta karbe

lambobinsa 7 na yabo na tseren Faransa wato Tour de France bayan an same shi da laifin amfani da kwayoyin kara

kuzari.

An baiwa ba Amurken kwanaki 21 ya daukaka kara kafin karbe lambar Olympics din amma bai daukaka ba.

Hukumar Tseren Keken ta Duniya ta karbe sakamakon dukkanin nasarorin da ya samu tun daga 1 ga watan Agusta

na 1998 kuma ta haramta masa shiga gasar tsere tsawon rayuwarsa bayan da Hukumar yaki da amfani da kwayoyin

kara kuzari ta Amurka (Usada) ta ayyana shi a matsayin hamshakin mai amfani da kwayoyin kuzari.

Ita ma Hukumar Yaki da Amfani da kwayoyin Kara Kuzarin ta Amurka ta haramta wa Arstrong din dan shekara 41

shiga wasan tseren keke har abada a kan abin da ta kira kwararriyar zambar amfani da kwayoyi mafi nasara da aka

taba gani a harkar wasanni a duniya.

Armstrong ya yi wata hira ta talabijin game da batun amfani da kwayoyin da Oprah Winfrey da ke shiri a Amurka.

Za a nuna hirar kashi biyu ranar Juma'a da kuma Asabar da karfe 02:00 na GMT.

Karin bayani