Fatan Habasha: Lashe Gasar Afirka

Tawagar 'yan wasan kwallon kafar Habasha
Image caption Tawagar 'yan wasan kwallon kafar Habasha na fatan baiwa Najeriya mamaki

Habasha ta kafa tarihi saboda kasancewa kasar da ta zo matsayi na biyu a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ba tare da ta lashe ko da wasa daya ba—kai, ba tare da ta ci ko da kwallo guda ba.

Hakan ya faru ne a karon farko na gasar a shekarar 1957, bayan da hukumomin kwallon kafa na Masar da Habasha da Afirka ta Kudu da Sudan suka kafa Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka, wato CAF.

Habasha ta samu zarafin buga wasan karshe ne na gasar bayan an dakatar da Afirka ta Kudu saboda ta ki saka 'yan wasa bakar fata; a nan kuma Masar ta lallasa tawagar 'yan wasan Habasha, wato Walya Antelpes, da ci hudu ba ko daya a Khartoum.

Sai dai kuma a wannan karon, shekaru talatin da daya tun bayan shigarta gasar, kasar, wacce aka dasa tushen gasar da ita, ta dawo tana kuma fatan yin rawar gani a Afirka ta Kudu.

A cewar shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Habasha (EFF) Sahilu Gebremariam, "Mu ne tushen wannan gasa, sai dai mun samu koma-baya; amma yanzu daukacin kasar na da karsashi.

"Wasan kwallon kafa ne wasan da Habashawa suka fi kauna. Mun yi suna a duniya wajen guje-guje, amma duk inda ka shiga—makarantu, da kauyuka, da ma tituna—za ka ga kwallon kafa ta fi farin jini a wajen jama'a".

Karsashin Habashawan dai ya ta'allaka ne a kan tawagarsu wacce ta ginu a kan kwazo da aiki tare.

An saka Habasha, wacce ta lashe Kofin Kasashen Afirka a 1962, a matsayi na 110 a jerin kasashen da suka yi fice a harkar kwallon kafa a duniya, da kuma matsayi na 31 a Afirka.

Ta kuma samu gurbi a gasar ta bana ne bayan ta yi waje da Benin da Sudan, wadanda ta bi har gida ta ba su kashi a wasannin share-fage.

Tun watan Nuwamban 2011 Sewnet Bishaw ke horar da 'yan wasan Habasha, amma tsohon kocinsu, Iffy Onuora, wanda ya jagoranci 'yan wasan tsakanin watan Yulin 2010 da Afrilun 2011, ya ce tun zamaninsa alamun ci gaban da aka samu suka fara bayyana.

"Ina alfahari da samar wa 'yan wasan kwarewa lokacin ina kocinsu. Na kware sosai wajen tsare-tsare da hada karfi-da-karfe, kuma na kan yi wa 'yan wasan huduba, al'amarin da ya sha bamban da abin da suka saba gani", inji Onuora.

Kusan dukkan 'yan wasan na Habasha dai masu wasa ne a cikin gida, daga kungiyoyin Dedebit, da Defence, da Saint George. Dan wasa daya kacal ke buga wasa a kasar waje—dan wasan na gaba, Saladin Said, na wasa ne a Gasar Premier ta Masar.

Onuora ya yi amanna cewa rashin ficen Habasha zai taimakawa 'yan wasan su bayar da mamaki a rukuninsu wanda ya kunshi masu rike da kambun gasar Zambia, da Najeriya, da Burkina Faso.

A cewarsa, "Adane Girma dan wasan gaba ne mai hazaka wanda ke kai hari yadda ya kamata, kai ka ce wani matashin Alan Shearer ne. Shi kuwa Alula Girma dan wasa baya ne mai kwari wanda zai iya taka leda a Ingila, Shimelis Bekele kuma in ya shiga fili sai abin da hali ya yi tamkar ko wanne shahararren dan wasa lamba goma".

'Yan wasan, wadanda suka zama gwarzaye a kasarsu bayan da suka yi nasara a wasannin share-fage, ba za su so su kare a matakin rukuni ba.

A cewar Adane Girma, mai shekaru 27, "Mun san Najeriya da Zambia suna da kyau sosai, amma fa kada su manta mun samu shiga gasar ce ta hanayr baiwa Sudan kashi. Kuma Sudan ta buga a Gasar Cin Kofin Afirka na bara.

"A baya muna da matsalar cin abokan hamayyarmu a wasannin da suke karbar bakuncinmu; amma yanzu wannan ya zama tarihi--mun nuna cewa mun samu ci gaba, saboda haka ma muna da damar samun gurbi a Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil a 2014".

'Yan wasan Habasha ba su taba shiga gasa mafi girma a duniya ta kwallon kafa ba, amma yanzu samun wannan dama abu ne da suke iya hangowa--shekaru hudu bayan da aka haramta musu buga wasannin share-fage saboda takunkumin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta kakaba musu sakamakon kin bin tsare-tsarenta.