Benitez ya fidda rai da Premier

rafeal benitez
Image caption Rafeal Benitez ya ce Chelsea za ta iya samun nasara a kan kowa

Kocin kungiyar Chelsea Rafeal Benitez ya ce ya fidda rai da kofin gasar Premier na bana.

Zakarun Turan na uku a gasar Premier su na bayan Manchester United ta daya da maki 11.

Kocin ya ce game da Premier ba ya jin za su iya daukar kofin amma kofin Capital One ya na nan, ga kofin kalubale da har yanzu akwai damar daukan sa ga kuma kofin Europa.

Ya ce duka wadannan kofuna Chelsea za ta iya samun nasara a kan kowa ta dauka.