Chelsea ta ci Arsenal 2-1

'yan wasan chelsea da arsenal
Image caption Chelsea ta yi nasarar farko a gida bayan wasanni 4

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sami nasara a kan Arsenal da ci 2-1.

Juan Mata ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a minti shida da fara wasa.

Chelsea ta kara ta biyu ne a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida, wanda Frank Lampard ya ci bayan da mai tsaron gidan Arsenal Wojciech Szczesny ya kayar da Ramires.

A minti na hamsin da takwas Theo Walcott ya ramawa Arsenal kwallo daya.

Wannan ya basu kwarin guiwa su ka yi ta kaiwa mai masaukinsu Chelsea hari amma ba su samu damar ramawa ba aka tashi 2-1.

Wannan shi ne karon farko da Chelsea ta sami nasara a gida a 2013 bayan wasanni hudu.

Karin bayani