Najeriya da Burkina Faso 1-1

stephen keshi
Image caption Stephen Keshi bai ji dadin yadda 'yan wasansa suka yi sakaci ba

Burkina Faso ta tashi 1-1 da Najeriya a karawarsu ta rukuni na uku, wato Group C.

Alain Traore ne ya jefa kwallon da Burkina Fason ta rama a dai-dai minti na 94 bayan cikar lokaci.

Su kuwa 'yan wasan Najeriya sun ci kwallonsu ne tun a minti na 23 ta hannun Emmanuel Emenike.

Alkalin wasa ya kori dan wasan Najeriya na baya Efe Ambrose saboda rike da ya yi bayan ya sami katin gargadi tun da farko.