Najeriya ta yi kunnen doki da Zambia

Najeriya ta yi kunnen doki da Zambia
Image caption Najeriya ta tashi 1-1 a wasanta na farko da ta buga da Burkina Faso

Golan Zambia Kennedy Mweene ya zira kwallo a bugun fanareti ana gab da tashi daga wasa abinda ya basu damar tashi 1-1 a wasansu da Najeriya a gasar cin kofin kasashen Afrika.

Mweene ya zira kwallon ne bayan alkalin wasa ya ce Ogenyi Onanzi ya tade Emmanuel Mayuka - hukuncin da ake ganin ya yi tsauri.

Tunda farko Najeriya ta zubar da fanareti lokacin da John Obi Mikel ya daki kararrawa a lokacin ana 0-0.

Emmanuel Emenike ne ya fara zirawa Super Eagles kwallonsu sai dai fanaretin da ake cece-kuce akai ya hanasu samun nasara.

Wannan wasa ya kara nuna yadda Zambia ke fuskantar koma-baya, idan aka yi la'akari da rawar da ta taka lokacin da ta lashe gasar a bara.

A daya wasan da aka buga a rukunin Burkina Faso ta lallasa Ethiopia da ci 4-0, kuma Burkina ce ke kan gaba a rukunin da maki hudu.

A yanzu dai rukunin a bude yake inda duka kasashen hudun na da damar tsallake wa zuwa zagaye na gaba.

Najeriya ta tashi 1-1 a wasanta na farko da ta buga da Burkina Faso, haka dai itama Zambia ta tashi a wasanta na farko da Ethiopia.

Karin bayani