Djokovic ya yi nasara a kan Berdych

novak djokovic
Image caption Novak Djokovic ya yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe

Novak Djokovic ya sami nasara a kan Tomas Berdych zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Tennis ta Australian Open.

Djokovic na daya a duniya a wasan tennis wanda kuma ya ke rike da kofin gasar ta Australian Open ya sami nasarar ne da maki 6-1 4-6 6-1 6-4 a cikin sa'oi biyu da minti 31.

Zakaran tennis din na duniya ya dawo wasa ne sa'oi 48 bayan fafatawar da ya yi ta tsawon sa'oi 5 da Stanislas Wawrinka da ya fitar, ya kuma sami galaba a kan Berdych din wanda ya ke matsayi na biyar a jerin gwanayen tennis na duniya.

Ana ganin Berdych ya yi tsammanin zai sami damar karya lagon Djokovic dan kasar Serbia ne a wasan ganin yadda zakaran na duniya ya yi sa'oi 5 da minti biyu kafin ya fitar da Stanislas Wawrinka, amma kuma hakan ba ta tabbata ba.

Yanzu Djokovic zai fafata da David Ferrer wanda ya fitar da dan kasarsa Spaniya Nicolas Almagro

Karin bayani