Tunisia ta ci Algeria 1-0

'yan wasan tunisia
Image caption 'Yan Tunisia sun yi sa'a a dai-dai karshen lokaci

Kasar Tunisia ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta ta Afrika ta Arewa Algeria da ci 1-0 a wasan rukuni na hudu wato Group D na gasar cin Kofin Afrika.

Dan wasan Tunisia Youssef Msakni shi ne ya ci kwallon a na dab da tashi daga wasan cikin minti na 90.

'Yan wasan Algeria sun fara wasan da kyau sai dai ba su sami nasarar cin wata kwallo da su ka samu dama ba a bayan minti 29 inda kwallon da Islam Slimani ya buga ta doki saman karfen ragar gidan Tunisia.

Da wannan nasara yanzu Tunisia ta bi bayan Ivory Coast wadda tun da farko ta ci Togo 2-1a rukunin na hudu.

Karin bayani