Mourinho ya hakura da La Liga

jose mourinho
Image caption Jose Mourinho ya ce zasu maida hankali kan wasu kofunan

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta Spaniya Jose Mourinho ya ce ya hakura da Kofin gasar La Liga na bana.

Mourinho ya ce abu ne da ba zai yuwu ba Real Madrid ta dauki kofin na Lig din Spaniyan a wannan kakar wasanni.

Real Madrid wadda ta dauki kofin a bara yanzu maki 15 ne tsakaninta da ta daya a gasar, Barcelona kuma maki 7 ne tsakaninta da ta biyu Atletico Madrid.

Kocin ya ce daukan kofin abu ne da ba zai yuwu ba saboda akwai tazara mai yawan gaske a tsakani.

Ya ce a don haka sai dai su maida hankali a kan wasu kofunan kamar Kofin Spaniyan na Copa del Rey (king's Cup) da kuma na Zakarun Turai.

Karin bayani