Tennis: Murray ya doke Chardy

Andy Murray
Image caption Andy Murray dan Birtaniya ne

Dan wasan Tennis din nan, Andy Murray ya doke Jeremy Chardy a zagayen dab da na kusa da na karshe, a gasar Australia Open.

Nasarar ta sa Murray kaiwa ga zagayen na kusa da na karshe a gasar da ake yi a Melbourne.

Wannan ne karo na hudu a jere da Murray ya samu nasarar kaiwa zagayen na kusa da na karshe a gasar ta Australia Open.

Sai dai kuma a bangaren mata, anyi waje da fitacciyar 'yar wasan tennis din nan Serena Williams.

Sloane Stephens ce ta doke Serena a zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar.