Ghana ta doke Mali da 1 - 0

'yan wasan Ghana na murnar nasarar da suka samu a kan Mali
Image caption 'Yan wasan Ghana na murnar nasarar da suka samu a kan Mali

Kasar Ghana ta yi hobbasa a gasar cin kocin nahiyar Afrikan da a halin yanzu ake yi a Afrika ta Kudu, inda ta doke Mali da ci daya da nema.

Hakan ya kai Ghana zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe a rukunin B, a wasan da suka yi a Port Elizebeth.

Mubarak Wakaso ne ya zura kwallon a yayin fenariti, bayan fara wasan da mintoci 38.

Seydou Keita ya zubar da wata dama ta zura wa Mali kwallo, inda ya wurga kwallon waje, bayan mai tsaron gidan Ghana ya shiga cikin fili ya bar raga ba kowa.

Kungiyar Ghana ta Black Stars dake son daga kofin nahiyar Afrika a karo na biyar, wanda na karshen da ta dauka tun shekarar 1982, ta san idan ta samu nasara a kan Nijar hakan zai zamo tabbacin samun shiga kungiyoyi takwas na karshe.

A ranar litinin mai zuwa ne kuma, Mali za ta kece raini da DR Congo a wasan rukunin B.