Kofin FA - Brentford da Chelsea 2-2

brentford da chelsea
Image caption Chelsea ba ta yi rashin nasara ba a wasanni 25 na gasar kofin FA

Kungiyar Kwallon Kafa ta Brentford dake rukunin kasa da Premier ta tashi 2-2 da kungiyar Chelsea ta Premier a gasar cin Kofin Kalubale na Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila FA.

Dan wasan Brentford, Trotta, shi ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea a minti na 42, amma kuma a minti na 55 Oscar ya rama wa Chelsea.

Bayan hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 73 Forrester ya ci Chelsea ta hanyar bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida.

Ana saura minti bakwai ne wa'adin wasan ya cika na minti 90 Fernando Torres ya ceto Chelsea ya rama kwallo ta biyu.

Yanzu za a sake wasan a nan gaba a gidan Chelsea, Stamford Bridge.

Karin bayani