Cape Verde ta ci Angola 2-1

angola cape verde
Image caption Cape Verde ta bi bayan Afrika Ta Kudu a rukunin farko

Kasar Cape Verde wadda a karon farko ta sami shiga gasar cin Kofin Afrika ta tsallake zuwa matakin wasan gab-da-na-kusa-da-na-karshe bayan da ta ci Anglo 2-1.

'Yan wasan na Cape Verde sun sami wannan nasara ne ta zuwa matakin kasashe 8 na gasar bayan da suka sami galaba daga baya a karawar tasu da takwarorin nasu na Angola.

'Yan Angolan sun sami damar jagaba a wasan ne tun a minti na 33 bayan da dan wasan baya na Cape Verde Neves ya ci kansu da kansu.

Saura minti 9 a tashi daga wasan 'yan Cape Verde da ake wa lakabi da Blue Sharks suka rama kwallon lokacin da dan wasansu na baya Fernando Varela ya ci da ka.

A minti na 90 ne kuma dan wasan Cape Verde da ya shigo daga baya Heldon ya jefa kwallo ta biyu a ragar Angola wadda ta basu damar zama na biyu a rukunin farko wato Group A , bayan Afrika ta Kudu ta daya a rukunin.

Karin bayani