Afrika ta kudu ta zama ta daya

afrika ta kudu
Image caption Afrika ta Kudu ta zama ta daya a rukunin farko

Kasar Afrika ta Kudu ta zama ta daya a rukunin farko, Group A, na gasar cin Kofin Kasashen Afrika bayan da ta yi canjaras 2-2 da kasar Morocco.

Issam El Adoua ne ya fara saka kwallo a ragar Afrika ta Kudu a minti 10 da fara wasan.

A minti na 71 kuma May Mahlangu ya ramawa Afrika ta Kudun kafin daga bisani Abdelilah Elhafidi ya ciwa Moroccon kwallo ta biyu a minti na 82.

Saura minti hudu ne kuma wa'adin wasan ya cika na minti 90 Sangweni ya rama wa Afrika ta Kudu kwallo ta biyu.

Da wannan sakamako Moroccon wadda sau biyu ta na zama kan gaba a lokacin karawar ta fice daga gasar saboda Cape Verde ta ci Angola 2-1.

Karin bayani