Man City ta musanta tafiyar Balotelli

mario balotelli
Image caption Mario Balotelli na nan daram a Man City in ji Mancini

Kungiyar manchester City ta musanta bayannan da kafafen yada labaran kasar Italiya suka watsa cewa Mario Balotelli na gab da komawa AC Milan.

Mataimakin kocin Manchester City David Platt ya ce babu inda Mario balotelli zai tafi wannan watan.

Haka shi ma mai magana da yawun kungiyar AC Milan Riccardo Coli ya bayyana rahotannin komawar dan wasan mai shekaru 22 kungiyarsa da cewa rade radi ne kawai.

An ruwaito kocin Manchester City Roberto Mancini ranar Juma'a yana cewa tun lokacin da Balotelli ya zo Ingila a 2010 ake cewa zai koma Italiya.

Ya ce ''dan wasan ba zai tafi ba, ba gaskiya ba ne maganar tafiyarsa, Mario yana nan, ba mu sami wata bukata ta neman sayensa ba ko kuma wasu 'yan wasan''.

Mancini dan shekara 48 ya nuna bacin ransa a kan rade radin tafiyar Balotellin yace Mario yana da sauran shekaru 3 a kungiyar kuma har yanzu yana bukatarsa.

Rade-Radi

Kafin wadannan bayanai dai rahotanni sun bayyana cewa dan wasan ya kammala shirinsa na barin Manchester City.

An ce Manchester City ta rage farashin da ta sanya a kan dan wasan zuwa Euro miliyan 23 bayan da ta yi watsi da tayin da Milan ta yi na Euro miliyan 29 da za ta biya a tsawon shekaru 6.

A maimakon haka ta rage ma sa farashi ta sanya wanda za a biya a cikin kankanin lokaci.

Zakarun gasar ta Premier sun kuma bukaci Milan ta biya kashi 15 cikin dari na kudin idan ciniki ya tabbata da Milan din kafin karshen wa'adin musayar 'yan wasa ranar Alhamis da daddare.

AC Milan din dai ta na son sayar da dan wasanta na baya Philippe Mexes domin ta yi tsimin kusan Euro miliyan 4 da rabi a shekara domin biyan kudin sayen Balotellin wanda shi kuma ya yarda a rage ma sa albashinsa na Euro dubu 129 a sati.

Tabarbarewar Dangantakarsa da Man City

Tsohon dan wasan na Inter Milan ya ci wa Man City kwallo daya ne kawai a bana a gasar Premier.

kuma mu'amullarsa da kocin kungiyar Roberto Mancini ta kara tabarbarewa bayan da su ka cukumi junansu a ya yin atisaye a farkon watan Janairu.

Wannan ya sa babban jami'in harkokin kwallon kafa na kungiyar Txiki Begiristain ya nemi sayar da dan wasan shekaru biyu da rabi da sayen shi daga Inter Milan a kan kudi Euro miliyan 29.

Duk da cewa dai har yanzu tana kasa tana dabo game da tafiyar dan wasan saboda irin bayanan dake fitowa daga bangarorin da abin ya shafa na kungiyoyin biyu da kuma wakilin dan wasan shi dai Balotelli ya bayyana aniyarsa ta komawa Italiya saboda haihuwar da aka yi masa ta farko.

Karin bayani