West Brom ta ki sayar da Odemwingie

Peter Odemwingie
Image caption Odemwingie na ganin ba lallai bane ya sake samun damar tayin sayensa ko musayarsa nan gaba

A karo na biyu kulob din West Brom ya yi watsi da tayin sayen dan wasan gaba, Peter Odemwingie da QPR ta yi.

A makon jiya ne dai Albion ta ki amincewa da tayin sayen dan Najeriyan, a kan kudi fam miliyan uku.

Ranar juma'ar da ta gabata ne dan wasan mai shekaru 31 ya nemi a yi musayarsa, matakin da ya baiwa kulob din nasa haushi.

"Kamar yadda muka sha fada, bamu da niyya ko bukatar sayar da manyan 'yan wasanmu". Inji daraktan kulob din Richard Garlick.

Ya kara da cewa "Tun da muka ki mu bada musayar Peter, ya fito ya bayyana matsayinsa ga 'yan jarida da kuma a shafinsa na Twitter."

"Matsayin da ya dauka wani abu ne na cikin gida da kulob din zai duba". A cewar daraktan.

Cikin abin da Odemwingie wanda aka sanya hannu a kwantiraginsa a shekarar 2010 a kan kudi fam miliyan biyu da rabi, ya rubuta a shafinsa na twitter sune, kulob din na bada uzuri ne kawai na rashin musayarsa, kuma dansa da matarsa na asibiti, halin da yake ciki na bata masa rai.

Inda ya kara da cewa tun a bara ya kamata ace ya mika bukatar musayarsa, inda ya jera sunayen kulob-kulob kamar Fulham da Newcastle da Wigan wadanda West Brom ta ki karbar tayinsu a game da shi.