Ghana za ta yi karon batta da Nijar

Filin wasa
Image caption Ghana da Nijar, kowanne na fatan doke dan uwansa a filin wasa na Nelson Mandela

A yau ne Kungiyar kwallon kafa ta Ghana za ta kara da takwararta ta jamhuriyar Nijar, a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Black Stars ka iya zama kan gaba a rukunin B, a wasannin da ake yi a Port Elizabeth.

Kungiyar ta fara ne da kafar dama, inda ta sami maki hudu kuma ta dara Mali da maki daya, yayin da ta fi DR Congo da maki biyu.

Hakan na nufin kasar na bukatar kunnen doki ne kawai, ta kasance cikin kasashe takwas na karshe a gasar.

Idan Ghana ta samu galaba a kan Nijar, ba za ta kece raini da mai masaukin baki Afrika ta Kudu ba, sai dai ta kara da Cape Verde a wasan gab da na kusa da na karshe a ranar Asabar mai zuwa.

Sai dai Nijar, wacce ta samu maki a karon farko a gasar a ranar Alhamis din data wuce, na da damar ci gaba da kasancewa a gasar muddin ta doke Ghana.