Ghana ta shiga mataki na gaba

'yan wasan ghana
Image caption Ghana ta zama ta daya a rukuni na biyu

Kasar Ghana ta samu nasarar shiga matakin wasan gab da na kusa da na karshe na gasar cin Kofin Kasashen Afrika bayan ta lallasa Nijar da ci 3-0.

Kyaftin din Ghana Asamoah Gyan wanda ya taka rawar gani sosai a wasan shi ne ya fara cin kwallon a minti 6 da shiga wasa.

A minti na 23 da fara wasan ne kuma sai Christian Atsu ya jefa kwallo ta biyu a ragar 'yan Nijar din.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma ana minti na 49 lokacin da Gyan ya kai hari da ka mai tsaron gidan Nijar Daouda Kassaly ya kade kwallon amma John Boye na Ghana ya jefa kwallon a raga.

Nijar din ta fice daga gasar yanzu wadda ita ce ta biyu da kasar ta taba zuwa amma kuma ko da kwallo daya ba ta taba ci ba.

Ita kuwa Ghana ta zama ta daya a rukuni na biyu wato Group B da maki 7 a wasanni 3 inda zata kara a wasan gab da na kusa da na karshe da kasar Cape Verde wadda ta zo ta biyu a rukuni na farko ranar 2 ga watan Fabrairu.

Karin bayani