Mali ta sha a gasar Kofin Afrika

'yan wasan mali
Image caption 'Yan wasan Mali sun yi canjaras amma sun tsallake gaba

Kasar Mali ta sami nasarar shiga matakin wasan gab da na kusa da na karshe na gasar cin Kofin Afrika bayan ta tashi 1-1 da takwararta ta Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo.

Dieumerci Mbokani na Congo shi ne ya fara saka kwallo a ragar 'yan Mali a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti 3 da fara wasan.

Mintuna goma sha daya baya ne kuma wato minti 14 a wasan sai Mahamadou Samassa ya ramawa Mali bayan da takwaransa Adama Tambouraya auna masa kwallon.

Yanzu Mali za ta kara da mai masaukin baki Afrka ta Kudu wadda ta zama ta daya a rukuni na daya Group A ranar 2 ga watan Fabrairu a wasan gab da na kusa da na karshe.

Ita kuwa Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ta fice daga gasar.

Karin bayani