Balotelli: AC Milan, Juventus sun gana da Man City

Mario Balotelli
Image caption Balotelli na da sauran shekaru uku a kwantiraginsa da Manchester City

Kulob din Manchester City ya tattauna da AC Milan da kuma Juventus a kan sayen dan wasan gaba, Mario Balotelli.

Sai dai Man City za ta sayar da dan wasan ne kawai, idan kulob din biyu dake Serie A sun cimma wasu abubuwan da City ke bukata.

City na son sayar da dan wasan dan kasar Italiya, mai shekaru 22 a kan kudi euro miliyan 24.

Kodayake kungiyar bata riga ta daga Balotelli don sayar wa ba, kuma ba za ta rage ko kwabo daga cikin albashinsa ba, idan har zai bar kulob din.

Sabanin abin da rahotanni ke cewa, Balotelli na cikin tawagar da suka tafi London don tattaunawa da QPR a ranar Talata.

Milan ce ta fara mika goron gayyata domin tattaunawa a kan dan wasa, yayin da daga bisani kuma Juventus ta tuntubi kulob din Man City game da batun neman sayen Balotelli.

A ranar Litinin din data gabata ne, mataimakin manajan kulob din City, David Platt yace Balotelli ba zai koma AC Milan a wannan watan ba.

Haka kuma manajan kulob din, Roberto Mancini a ranar Juma'ar da ta wuce, ya jaddada cewa Balotelli ba zai bar kulob din ba.