Ferdinand ya koma Bursaspor

anton ferdinand
Image caption Anton Ferdinand zai yi wasa a Turkiyya har karshen kakar bana

Dan wasan baya na Queens Park Rangers Anton Ferdinand ya tafi kungiyar Bursaspor ta Turkiyya a matsayin aro.

Ferdinand dan shekara 27 zai karasa sauran lokutan kakar wasanni ta bana a Turkiyya kafin ya yanke shawara a kan matsayinsa a gaba.

Dan wasan ya koma QPR ne daga Sunderland a 2011 bayan da ya taka rawar gani a kakar wasanni ta bara, ya sami koma baya inda ba a sa shi a wasa sosai.

Tsohon dan wasan na West Ham bai buga wani wasan Premier ba tun daga farkon lokaci tun bayan wasan da su ka yi da West Brom da kungiyarsa ta sami nasara ranar 26 ga watan Disamba.

Ferdinand wanda ya buga wasan Kofin Kalubale na FA ranar Asabar da su ka yi da MK Dons wanda aka ci su 4-2 ya bi sahun tsohon mai tsaron gidan Ingila ne Scott Carson zuwa klub din na Bursaspor.

Kocin QPR Harry Redknapp ya na kokarin sayen sababbin 'yan wasa kafin karshen wa'adin musayar 'yan wasa ranar Alhamis, kuma zai rasa Ryan Nelsen ma wanda zai kama aiki a matsayin kocin Toronto a wannan makon.

A watan Satumba aka dakatar da kyaftin din Chelsea John Terry daga buga wasanni 4 da kuma tarar fam 220, 000 saboda cin mutuncin Ferdinand ta hanyar nuna wariyar launin fata a lokacin wasan QPR da Chelsea a watan Oktoba na 2011.