Zambia za ta kara da Burkina Faso

'Yan wasan Zambia
Image caption 'Yan wasan Zambia dauke da kofin da suke kare wa

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Zambia dake kare kambunta, za ta kece raini da Burkina Faso a gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Kuma idan Zambia na so ta samu zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar, to dole ta doke Burkina Faso a karawar da za su yi a Afrika ta Kudu.

Yayin da ita kuma Burkina Faso take bukatar yin kunnen doki kawai, ta samu ketara wa zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe.

A taka ledar da kasashen biyu za su yi da yammacin yau, kungiyar Burkina Faso za ta yi wasa ba tare da mai tsaron gida, Abdoulaye Soulama ba, wanda aka haramtawa yin wasanni biyu a gasar.

Kungiyar kwallon kafa ta kasar dai na fatan dan wasan tsakiyarta, Alain Traore zai ci gaba da nuna hazaka a wasan.

Ita kuwa Zambia, Burkina Faso bata taba doke ta ba, a karawar da suka yi sau biyu, a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a baya.