Kofin Afrika : Togo ta tsallake gaba

'yan wasan togo
Image caption 'Yan wasan Togo sun kafa tarihi a gasar Kofin Afrika

Kasar Togo ta samu nasarar tsallake wa zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe a karon farko a tarihinta na gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Afrika, bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Tunisia.

'Yan wasan Togon ne su ka fara jefa kwallo a ragar Tunisia a minti na 13 bayan da Emmanuel Adebayor ya tura wa Gakpe kwallon wanda shi kuma ya bai yi wata-wata ba ya aika ta raga.

A minti na talatin ne kuma 'yan Tunisia su ka rama kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida ta hannun Khaled Mouelhi.

Tunisian ta rasa damar samun nasara a wasan wanda ya zama wajibi ta ci domin wuce wa zuwa mataki na gaba bayan da Mouelhin ya barar da wani bugun fanaretin da suka samu.

Da wannan nasara To go ta zama ta biyu a rukuni na hudu wato Group D na gasar ta Afrika inda zata kara da Burkina Faso ranar Lahadi 3 ga watan Fabrairu.

Karin bayani