Balotelli ya koma kulob din AC Milan

Mario Balotelli
Image caption Balotelli ya taimakawa City a gasar premier League na bara

Kulob din kwallon kafa na AC Milan ya tabbatar da sayen dan wasan gaba na Manchester City, Mario Balotelli.

Dan wasan mai shekaru 22, ya amince da kwantiragin shekaru hudu da rabi a kulob din Italiyan, bayan an kammala duba lafiyarsa a ranar Laraba.

AC Milan ta sayi dan wasan ne a kan kudi fam miliyan 19.

"Har abada ba zan iya cire son Man City daga zuciya ta ba, kulob ne mai kyau wanda kuma ke da kyakkyawar makoma." Inji Balotelli.

Ya kara da cewa "Ina godiya garesu game dukkan goyon bayan da suka bani, kila wata rana za mu sake haduwa da juna."

A shekarar 2010 City ta sayo dan wasan daga kulob din Inter Milan, a kan kudi fam miliyan 24, kuma ya ciwo wa City kwallaye 30 a wasa 80 da yayi a kulob din.

Dan wasan dai yayi bankwana da ragowar 'yan wasan Man City a wata liyafar cin abinci da aka shirya, gabannin kunnen doki da kulob din yayi a taka ledarsu da QPR.