Ashley Cole zai shiga tarihi a Ingila

ashley cole
Image caption Ashley Cole zai shiga cikin jerin fitattun 'yan wasan Ingila

Dan wasan Chelsea Ashley Cole zai kafa tarihin bugawa Ingila wasa karo na 100 a karawar da kasar za ta yi da Brazil.

Cole wanda ya fara bugawa Ingila wasa ranar 28 ga watan Maris na 2001a haduwarta da Albania ya na cikin 'yan wasa 24 da kocin kasar Roy Hodgson ya zaba domin fafatawa da Brazil.

Dan wasan zai zama na bakwai cikin wadanda suka kafa tarihin yi wa Ingila wasa har sau dari daya.

Zai shiga sahun Gerrard da Billy Wright da Bobby Charlton da Bobby Moore da David Beckam da kuma Peter Shilton.

Sauran 'yan wasan da kocin ya zaba domin bugawa Ingila wasan da Brazil sun hada da Frank Lampard da Jack Wilshere da Micheal Carrick da Tom Cleverly da Leon Osman da kuma kyaftin Steven Gerrard.

Duk da rauninsa Jermaine Defoe shi ma ya samu shiga tare da Wayne Rooney da Danny Welbeck da sabon matashin dan wasan Liverpool Daniel Sturridge.

Kamar yadda aka yi tsammani Hodgson bai dauki Raheem Sterling da Jonjo Shelvey da Wilfred Zaha ba, a maimakon haka an sanya sunayensu cikin wadanda za su buga wasan Ingilan na 'yan kasa da shekara 21 da za su yi da sweden ranar 5 ga watan Fabrairu.

Kocin ya kuma yi bazatta wajen daukar masu tsaron gida biyu kawai - Joe Hart da na kungiyar Bermingham Jack Butland