Ranar karshe ta musayar 'yan wasa

  • 31 Janairu 2013
Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA

Yau Alhamis ne ranar karshe ta musayar 'yan wasan kwallon kafa a tsakanin kulob-kulob na kasashen duniya.

Kuma damar musayar 'yan wasan za ta kawo karshe ne da misalin karfe goma sha daya na dare, agogon GMT.

Abin da ya sa kungiyoyi ke hanzarin karshe na ganin sun kammala sanya hannu a kan kwantiragin 'yan wasa masu fita da shiga cikinsu.