Najeriya za ta raba raini da Ivory Coast

Stephen Keshi
Image caption Kocin Najeriya, Stephen Keshi, yana da kwarin gwiwa

Daya daga cikin wasannin zagayen gab da na kusa da karshe na ranar Lahadi a Gasar Kwallon Kafa ta Cin Kofin Kasashen Afirka shi ne na Najeriya da Ivory Coast.

A wasanni biyar tsakanin kasashen biyu a gasar cin kofin na Afirka, kowacce ta samu galaba a wasanni biyu yayin da aka tashi canjaras a guda.

Najeriya dai ta kawo wannan matakin ne bayan ta tashi kunnen doki a wasanninta da Burkina Faso da Zambia kafin ta doke Habasha da ci biyu da nema.

Kocin tawagar Najeriya ta Super Eagles, Stephen Keshi, ya ce:

“Muna da kwarin gwiwa, mun san cewa za mu tabuka abin a-zo-a-gani a wannan gasar, amma kuma wani abin kunya shi ne yadda [al’ummar] kasata ba ta da kwarin gwiwa a kan tawagarta—abin takaici ne a yanke kauna a kan ’yan wasan.

“Ko da ma da Brazil za mu fafata, bai kamata ba a sa ran kawai kashi za mu sha, saboda wannan abu zai sanyaya gwiwar ‘yan wasa”.

A nata bangaren dai, Ivory Coast ta samu nasara a wasanninta biyu na zagayen farko sannan ta tashi biyu da biyu tsakaninta da kasar Algeriya.

Wasan zai kasance zakaran gwajin dafi ga kocin kasar, Sabri Lamouchi, wanda ake ganin ’yan wasansa sun fin na sauran kasashe a gasar gogewa.

Dan wasan Ivory Coast Max Gradel ya yi tsokaci a kan karawar:

“Duka ’yan wasan tawagar sun fuskanci abu guda, saboda a wancan karon mun kai wasan karshe amma ba mu samu nasara ba.

“A wannan karon muna da kwarin gwiwar cewa za mu samu nasara, kuma za mu fara ne da wannan wasan da Najeriya, har mu kai wancan matakin”.

Wasa na biyu shi ne tsakanin Togo da kasar Burkina Faso. Burkina Faso za ta buga wannan wasan da kwarin gwiwa musamman saboda a bara ta lallasa Togo da ci uku da nema a wasan sada zumunta.

Tuni dai Ghana da Mali suka tsallake zuwa zagayen kusa da karshe, bayan sun samu nasara a karawar da suka yi a zagayen gab da na kusa da karshe.

Ita dai Ghana ta samu gurbinta ne bayan ta casa kasar Cape Verde da ci biyu da nema.

Mubarak Wakaso ne ya ciwa Black Stars kwallaye biyu, ta farko a bugun fanariti, ta biyu kuma bayan cikar minti na casa’in na wasa, golan Cape Verde ya nausa ciki bayan kasarsa ta samu kwana, sai aka cillo kwallon ciki, Wakaso kuma ya zura kwallon babu gola a cikin raga.

Kenan an fitar da Cape Verde daga gasar.

Ita kuwa Mali, da kyar da jibin goshi ta samu nata gurbin saboda sai a bugun fanariti ta samu galaba a kan mai masaukin baki Afrika ta Kudu.

Bayan sun tashi kunnen doki, an kara mintuna 30, amma duka kasashen biyu wato suka kasa zura kwallo har sai da bugun fanariti ya raba musu gardama.

Karin bayani