Har yanzu muna sa rai da Premier - Mancini

roberto mancini
Image caption Roberto Mancini ya ce har yanzu da sauran tafiya a Premier

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce har yanzu ba su fidda rai ba da Premier duk da cewa maki tara ne tsakaninsu da Manchester United.

Kocin ya furta hakan ne bayan karawar da City din ta yi da Liverpool a gidanta Etihad wadda aka tashi 2-2.

Dzeko ne ya fara jefa kwallo a ragar Liverpool a na minti 23 da wasan sannan kuma Sturridge ya rama minti 6 tsakani.

Ana minti na 73 ne kuma Gerrard ya mulmulo wata kwallo daga nesa wadda bata zame ko ina ba sai cikin ragar Manchester City.

Amma kuma wannan murna ba ta yi karko ba domin a minti na 78 ne kawai Manchester City ta rama kwallon ta biyu ta hannun Aguero.

Mancini ya ce ''har yanzu da sauran tafiya a gasar ta Premier wani klub din zai iya yin kuskure.

Yanzu kila muna bukatar mu yi nasarar ci wasanninmu 13 duka, idan kuma ba haka ba mu ci 11 ko 12.''

Mancini ya kara da cewa ''wannan wasan kwallon kafa ne kuma hakan ka iya faruwa.

Kamar yadda ta kasance a bara inda muka farfado daga bambancin maki 8 a wasanni 6 na karshe.''

Ya ce yanzu a kwai sauran wasanni 13 da suka rage kuma hankalin Manchester United zai rarrabu saboda zata yi wasan Premier da na Kofin Kalubale da kuam na Zakarun Turai, kakar wasannin ta na da tsawo akwai sauaran watanni 3 kuma muna da kwarin guiwa.