Balotelli ya fara AC Milan da sa'a

mario balotelli
Image caption Sayen Mario Balotelli, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu

Mario balotelli ya fara wasa a Kungiyar AC Milan da sa'a inda ya ci kwallaye 2 a karawarsu da Udinese.

A ranar Alhamis ne dan wasan mai shekaru 22 da AC Milan ta saye shi fam miliyan 19 daga Manchester City ya koma kungiyar ta Italiya.

A lokutan karshe ne aka sa dan wasan bayan Giampaolo Pazzini ya ji rauni a wasan amma kuma bai yi wata-wata ba wajen ciwa kungiyar kwallo kafin kuma ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya baiwa klub din nasara 2-1. Gianpiero Pinzi ne ya ramawa bakin kwallonsu bayan hutun rabin lokaci.

Balotelli ya ci wa Manchester City kwallaye 30 a wasanni 80 da ya buga bayan da klub din ya sayo shi daga Inter Milan a 2010 a kan kudi fam miliyan 24 amma aka sayar da shi a karshen lokacin musayar 'yan wasa na watan Janairu.

Karin bayani