Balotelli ya kushe Ingila

mario balotelli
Image caption Mario Balotelli ya kushe rayuwar Ingila

Tsohon dan wasan Manchester City Mario Balotelli ya kushe yanayin rayuwa a Ingila bayan da ya koma kungiyar AC Milan ta Italiya a kan kudi fam miliyan 19.

Ranar Juma'a ne sabuwar kungiyar tasa ta gabatar da shi a bainar manema labarai kuma bai yi wani kawaici ba lokacin da aka tambaye shi abun da ya keso da abun da ba ya so game da Ingila.

Yace ai ba bu wani abu da ya ke jin dadinsa a Ingila da kuma zai yi kewarsa kamar lokacin da ya ke zuwa fili domin atisaye sai kuma takwarorinsa 'yan wasan City da kuma kocinsa kawai.

Game da abubuwan kaico kuwa dan wasan ya ce ai komai ma kama daga 'yan jarida da yanayi da abinci da kuma yadda ka ke tukin mota.

Mario Balotelli dan shekara 22 ya amince da kwantiragin shekaru hudu da rabi ne da zakarun Italiyan AC Milan bayan zamansa a Manchester United na shekaru biyu da rabi da ya ci musu kwallaye 30 a wasanni 80.

Sau da dama yana samun kansa cikin dambarwa da takaddama a filin wasa da kuma a wajen filin tsawon lokacin zamansa a Man City.

Sai dai dan wasan ya shedawa manema labarai a Milan cewa ya kwammace ya yi wasa maimakon ya rinka maganganu.

Ya ce ''burina ne daman na zama dan wasan AC Milan, yanzu ina matukar farin ciki.''

''Ina kusa da iyalina da abokanaina, Manchester ba ta da nisa amma kuma bata kai Milan kusanci ba.''

Da aka tambaye shi ko wata rana zai so ya koma gasar Premier,sai ya ce bai sani ba.

Karin bayani