Ashley kwararren dan wasan baya - Stuart

Ashley Cole
Image caption Ana fargabar cewa 'yan kallo ba za su yi wa Ashley sowa na marhaba ba a Wembley, saboda munanan labarai da aka ta yi a kansa

An bayyana dan wasan Ingila, Ashley Cole a matsayin kwararren dan wasan bayan da kungiyar kwallon kafa ta Ingila ta taba samu.

Manajan kulob din Stuart Pearce ne ya bayyana hakan.

Ana sa ran dan wasan zai cimma samun nasarar buga wasanni 100, a wasan sada zumuncin da Ingila za ta yi da Brazil, a filin wasa na Wembley a ranar Laraba.

Idan ya kasance cikin wadanda za su murza ledar, dan wasan mai shekaru 32 dake wasa a kulob din Chelsea, zai zama dan wasan Ingila na bakwai da ya taba buga yawan wasannin.

"A ganina shi ne dan wasan baya da ya fi kowa da ya taba bugawa Ingila wasa, iya gaskiyar maganar kenan, a iya sanina." a cewar Pearce.

"Mutum ya buga wa kasarsa wasa har sau dari, wannan ba karamin abu bane."

Haka kuma manajan na ganin ba a yabawa bajintar Cole, saboda haka zai je wasan da za su yi da Brazil, domin jinjina wa Cole a lokacin da za a kira sunansa domin taka leda.