Hodgson ya tabbatar Cole zai yi wasa

ashley cole
Image caption Ashley Cole zai shiga tarihin Ingila

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce dan wasan baya Ashley Cole zai buga wasan sada zumunta da kasar za ta yi da Brazil a Wembley ranar Laraba da zai zama karo na 100 cif da ya ke yi wa kasar wasa.

Cole mai shekaru 32, a watan Maris na 2001 ya fara bugawa Ingila wasa a karawarta da Albania kuma zai zama dan wasanta na bakwai da ya cimma wannan nasara ta buga wasa sau 100.

Hodgson ya ce zai duba ya ga yadda zai yi da Leighton Baines wanda ke wasa a matsayi daya da Cole, da shi ma tauraruwarsa ke haskawa a yanzu.

Sai dai kuma kocin na Ingila ya kawar da yuwuwar cewa Cole ne zai yi wa Ingila kyaftin a wasan da Brazil maimakon kyaftin din ta na ainahi Steven Gerrard.

Hodgson ya ce bai ga dalilin da zai sa kyaftin din ya bari wani ya jagoranci kungiyar ba.

Wasan da Brazil na shirin tunkarar karawar da Ingila zata yi ne ta neman zuwa gasar cin kofin Duniya da San Marino da Montenegro.

Hodgson zai kuma fuskanci matsalar rashin Jermain Defoe da Daniel Sturridge da kuma Micheal Carrick wadanda suka ji rauni.

Ana ganin rashin 'yan wasan na gaba biyu zai sa kocin ya yi amfani da Theo Walcott a tsakiyar gaba mai makon gefe da ya saba bugawa.

Karin bayani