Ferdinand na so ya dawo bugawa Ingila

rio ferdinand
Image caption Rio Ferdinand na son ci gaba da yiwa Ingila wasa

Rio Ferdinand ya ce zai amsa kira kai tsaye idan aka sake gayyatarsa kungiyar 'yan wasan Ingila ta kasa.

Ferdinand dan shekara 34 bai bugawa Ingila wasa ba tun watan Yuni na 2011 kuma ba a sa shi cikin tawagar 'yan wasan Ingila da suka shiga gasar Kofin Turai ta 2012 ba karkashin kulawar Roy Hodgson.

Ferdinand wanda ya bugawa Ingila wasanni 81 bai sake buga mata wani wasa ba tun na neman shiga gasar Kofin Turai da Switzerland a filin Wembley.

Dan wasan shi ne wani babban dan wasa da ba a kirawo ba a tawagar 'yan wasan Ingila ta gasar cin Kofin Turai na 2012 inda kocin kasar Roy hodgson ya ce rashin gayyatara tasa hukunci ne da ya shafi kwallon kafa kawai amma ba wani abu na daban ba.

Karin bayani