FIFA na neman bayani kan satar gida

tutar fifa
Image caption FIFA na neman kawar da sarkakiya a dokar wasa.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya,FIFA, ta bukaci 'yan Hukumar da ke yin dokokin wasan da su fayyace ka'idar dokar satar gida a lokacin wasa.

FIFA ta na son a fayyace cewa ko dan wasan da yake yankin satar gida ya na daukar hankali a lokacin wasa ko kuma ba ya yi.

A halin yanzu doka ta 11 ta ce dan wasan da yake yankin satar gida na iya daukar hankali ta hanyar motsinsa wadda a fahimtar alkalin wasa ka iya yaudarar dan wasan daya kungiyar.

A kan haka Hukumar ta Kwallon Kafa ta Duniya ta ke son a saukaka ma'anar dokar ta yadda alkalin wasa ba zai yi wata fassara ta dabam ba wadda za ta zo dai dai da ra'ayinsa.

A ranar 2 ga watan Maris ne 'yan Hukumar dokokin wasan kwallon kafar ta duniya, IFAB, za su y taro a Edinburgh ta Ingila inda za su tattauna a kan amfani da fasahar nan ta tantance shigar kwallo raga wadda aka jarraba ta gasar cin Kofin Duniya na kungiyoyi a Japan a watan Disamba da ya wuce.

A yayin taron ne Hukumar ta FIFA ta ke son 'yan Hukumar su fayyace dokar ta satar gida.

Karin bayani