Ana sabon bincike a kan Armstrong

lance armstrong
Image caption Lance Armstrong ya furta cewa ya yi amfani da kwayoyi

Shahararren dan tseren keken nan na duniya dan Amurka Lance Armstrong yana fuskantar sabon bincike bayan da ya ambata cewa ya yi amfani da kwayoyin kara kuzari.

Kafafen yada labaran Amurka sun bayyana cewa Armstrong ka iya fuskantar sababbin tuhumce tuhumce na aikata miyagun laifuka.

Wannan sabon bincike dai ya biyo bayan kalaman da dan tseren keken ya yi ne a wata hira da Oprah Winfrey.

A hirar ya furta da kansa cewa ya yi amfani da kwayoyin kara kuzari a dukkanin gasa bakwai da ya shiga ta tseren Keken Faransa wato Tour de France.

Sai dai kuma Maigabatar da kara Andre Birotte wanda ya jagoranci binciken da aka yi wa dan tseren keken a baya ya ce shawarar da aka yanke ta baya cewa ba za a gurfanar da Armstrong gaban shari'a ba na nan daram.

Karin bayani