Balotelli : Berlusconi ya nuna wariya

mario balotelli
Image caption Mario Balotelli ya fara gamuwa da ce-ce-ku-ce a Italiya

An zargi mataimakin shugaban kungiyar AC Milan da amfani da kalaman wariyar launin fata a kan sabon dan wasansu Mario Balotelli.

Kafofin yada labarai na kasar Italiya sun ce Paolo Berlusconi ya furta kalaman ne a wurin wani taron siyasa inda ya gayyaci mahalatta taron su je su kalli wasan sabon dan wasan da klub din ya saya daga Manchester City a kan fam miliyan 19.

An dauki bidiyon Berlusconi wanda dan uwan shugaban kungiyar ne Silvio lokacin da ya ke yin kalaman aka yada a shafin intanet na jaridar La Repubblica, abin da ya sa aka rinka sukan lamirinsa.

A kalaman nasa Paolo Berlusconi ya bayyana Balotelli a matsayin bakar fatar kungiyar.

Karin bayani