Najeriya ta shiga wasan karshe

'yan wasan najeriya
Image caption 'Yan wasan Najeriya sun yi rawar gani

Najeriya ta tsallake zuwa wasan karshe na gasar cin Kofin Kasashen Afrika bayan ta yi galaba a kan Mali da ci 4-1.

A minti na 25 ne dan wasan Najeria Echiejile ya fara jefa kwallo a ragar 'yan Mali, minti biyar tsakani kuma Brown ya sake cin ta biyu.

Gab da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma Najeriya ta ci kwallo ta uku a bugun fallen daya inda dan wasan Mali Sissoko ya ci kansu bayan da kwallon ta buge shi ta shiga raga.

Ahmed Musa wanda ya canji Victor Moses ya jefawa Najeriya kwallo ta hudu a minti na 60.

Sai dai kuma a minti na 75 Diarra ya ci wa Mali kwallonta daya.

Yanzu Najeriya za ta kara da kasar da za ta yi nasara tsakanin Ghana da Burkina Faso a wasan karshe.

Rabon Najeriya da zuwa wasan karshe na gasar cin Kofin Afrika tun shekaru 13 da su ka wuce