Louis Saha zai koma Lazio

louis saha
Image caption Louis Saha ya ci kwallaye 147 a Ingila

Tsohon dan wasan Sunderland Louis Saha na gab da komawa kungiyar Lazio ta kasar Italiya ba tare da klub din na Serie A ya biya tsohuwar kungiyar wani kudi ba.

Saha tsohon dan wasan kasar Faransa mai shekara 34 ya koma Sunderland ne a watan Agusta bayan da Tottenham ta sake shi.

A watan Janairu ne Sunderland ta saki dan wasan bayan ya yi mata wasanni 14.

Saha ya taba yi wa kungiyar Newcastle da Fulham da Manchester United da kuma Everton wasa.

Karin bayani