Jermain Defoe ya yi rauni

jermain defoe
Image caption Jermain Defoe ba zai yi wasa ba tsawon mako uku

Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta Ingila Andre Villas-Boas ya tabbatar cewa dan wasansu Jermain Defoe ya ji rauni a idon sawunsa kuma ba zai yi wasa ba tsawon mako uku.

Defoe mai shekaru 30 ya ji raunin ne alokacin wasansu da West Brom ranar Lahadi, wanda hakan ya sa Tottenham din ta zama ba ta da wani kwararren dan wasan gaba.

Sai dai kocin ya ce Emmanuel Adebayor wanda bai samu damar buga klub din wasanni hudu ba saboda gasar wasannin Kofin Afrika zai dawo wasa a lokacin karawarsu da Newcastle ranar Asabar.

Defoe ya fara kakar bana da sa'a inda ya ci wa Tottenham kwallaye 14 a wasanni 26.

Sai dai kuma fafatawarsu da West Brom karo na shida ke nan ana sa shi a wasa amma bai ci kwallo ba.