Dokar tsuke bakin aljihu a Premier

manchester city
Image caption Manchester City ta dauki Premier bayan Sheik Mansour ya saye ta

Gasar Premier ta bullo da tsarin takaita kudaden da kungiyoyin wasa ke kashewa.

A bisa tsarin nan da shekaru uku ba za a bari kowana klub daga cikin guda 20 na Premier din ba ya yi asarar da ta wuce ta fam miliyan 105.

Sannan kuma daga kakar wasanni ta 2013-14 dole ne kungiyoyin su tsaida iyakar albashin 'yan wasa.

An bullo da dokokin ne domin tabbatar da dorewar kungiyoyin ta fannin kudade don gudun durkushewarsu.

Shugaban hukumar gasar ta Premier Richard Scudamore ya ce duk klub din da ya saba dokar takaita asarar ta fam miliyan 105 din za a yi ma sa hukunci na rage maki.

Daga cikin kungiyoyin gasar ta Premier 20 Manchester City da Chelsea da Liverpool ne kawai su kayi asarar sama da fam miliyan 105 a shekaru uku da suka gabata kamar yadda alkaluma su ka nuna.

Karin bayani