Keshi ya jinjina wa Super Eagles

Stephen Keshi
Image caption Keshi ne na biyu da ya lashe gasar a matsayin dan wasa da kuma koci

Kocin Najeriya Steven Keshi ya jinjina wa 'yan wasansa bayan da suka doke Burkina Faso da ci 1-0 domin zamowa zakarun kwallon Afrika a karon farko tun shekara ta 1994.

Tsohon kyaftin din na Super Eagles ya zamo mutum na biyu a tarihi da ya lashe gasar a matsayin dan wasa da kuma koci bayan dan kasar Masar Mahmoud El Gohary.

Haka kuma shi ne koci bakar fata na farko da ya lashe gasar tun shekara ta 1992.

"Ina matukar alfahari da abinda 'yan wasa na suka yi a wannan gasar," a cewar Keshi.

"Sun taka rawar gani sannan sun mayar da hankali sosai a kan wasan. Suna da kwarewa sosai."

Keshi, wanda ya jagoranci Najeriya ta lashe gasar a shekaru 19 da suka gabata, ya kara da cewa: "Lokacin da na karbi wannan aiki shekara daya da rabi da ta wuce, fatana shi ne na samar da wata tawaga da 'yan Najeriya za su yi alfahari da ita.

"Har yanzu bamu cimma hakan ba amma muna kan hanya kuma ina farin ciki da haka."

Sunday Mba ne ya zira kwallon a minti na 40 kuma Keshi ya ce ba zai iya bayyana yadda ya rinka ji ba a lokacin da wasan ya zo karshe.

Karin bayani