Chile Open : Nadal a wasan karshe

rafeal nadal
Image caption Rafeal Nadal ya na ci gaba da farfadowa

Rafeal Nadal ya kai zuwa wasan karshe na gasar wasan tennis ta Chile Open bayan ya yi nasara a kan Jeremy Chardy dan kasar Faransa da maki 6-2 6-2.

Tsohon na daya a duniya a wasan tennis Nadal, mai shekara 26 wanda ya yi watanni bakwai ya na jiyyar ciwon guiwa ya fitar da abokin karawar tasa ne a cikin mintuna 64.

Da wannan nasara zai yi karawar karshe da na 73 a duniya Horacio Zeballos dan Argentina wanda ya fitar da Carlos Berlocq shi ma dan Argentina.

Haka kuma Nadal ya kai wasan karshe na mutum bibbiyu wanda zai hadu da Juan Monaco dan Argentina su kara da Paolo Lorenzi da Potito Starace 'yan Italiya.

Wannan ce gasa ta farko da Nadal ya ke wasa tun bayan da Lukas Rosol dan kasar Czech ya fitar da shi a zagaye na biyu na gasar Wimbledon a watan Yuni.

Karin bayani