Doke Man City ya sa muka yi sauyi - Ferguson

Manajan kulob din Manchester United
Image caption Manajan kulob din Manchester United

Manajan kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya tabbatar da cewa sauyin da ya yi wa kulob din, ya biyo bayan lallasa Manchester City da Southampton ta yi.

Hakan ya zo ne gabannin karawar Machester United da Everton.

Ferguson ya sanar da shirin yin wasu sauye-sauye bakwai.

Inda ya kara da cewa "A lokacin da naga sakamakon wasan a ranar Asabar, na fahimci muhimmancin karawar da za mu yi da Everton."

A ranar asabar ne, a filin wasa na St. Mary Southampton ta doke Man City da ci 3 da daya, abin dake nufin, idan Man U ta doke Everton da ci 2 da nema, kulob din zai zama yana da maki 12, kuma yana saman teburin premier League.