Mun daidaita da hukumar NFF - Keshi

Nigeria
Image caption Rabon da Najeriya ta lashe gasar ta cin kofin Afrika tun 1994

Kocin Super Eagles na Najeriya Steven Keshi ya ce ya warware matsalar dake tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta kasar NFF, wacce tasa ake yada rahotannin cewa yayi murabus.

"Duk da cewa ina da korafi kan wasu abubuwa da suka faru a lokacin gasar tsakani na da shugabannin NFF - tuni muka tattauna da wadanda lamarin ya shafa.

A yanzu ina bayyana cewa na sauya matsayina, kuma na yanke shawarar ci gaba da aikina," a cewar sanarwar dauke da sa hannun Keshi.

Tun da farko rahotanni sun bayyana cewa Keshi ya yi murabus daga mukamin na sa ne jim kadan bayan da Super Eagles ta lashe kofin ranar Lahadi, sakamakon barazanar da hukumar ta NFF ta yi na korarsa a farkon gasar - lokacin da tawagar kasar ke tangal-tangal a rukunin C.

Sai dai NFF ta ki amincewa da takardar murabusdin da ya mika mata bayan da suka doke Burkina Faso a wasan karshe.

Steven Keshi ya yabawa ministan wasanni na Najeriya Mallam Bolaji Abdullahi saboda rawar da ya taka wurin warware sabanin da aka samu.

Karin bayani